Lahadi 26 Yuli 2026 - 21:41
Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) Ya Kai Ziyarori ga Dangi da Fitattun Malaman Addini a Zariya

Hauza / Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, ya ci gaba da gudanar da ziyarorinsa a garin Zariya, inda ya kai ziyara gidajen wasu daga cikin dangi, fitattun malaman addini da tsoffin abokan arziki. A yayin ziyarar, ya jajanta wa iyalan marigayi Malam Ƙasim, Limamin Zariya, tare da yi masa da kuma dukkan muminan da suka rasu addu'ar rahama da gafara.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa, Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) a karon farko tun bayan dirar masa da gwamnatin Najeriya ƙarƙashin jagorancin Manjo Janar Muhammadu Buhari (L) a shekarar 2015, a ranar Lahadi, 11 ga watan Safar 1448 Hijira (26 ga Yuli, 2026), ya yi ziyarce-ziyarcen al'umma a garin Zariya, inda ya kai ziyara gidajen wasu daga cikin dangi da fitattun mutane da aka sani a wannan birni.

Wurin farko da Jagoran ya ziyarta shi ne gidan ta'aziyyar marigayi Malam Ƙasim, Limamin Zariya, da ke Unguwar Juma. A yayin ziyarar, ya jajanta wa iyalan mamacin, sannan ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa zunubansa, Ya ba shi matsayi mafi girma a Aljannatul Firdausi. Haka kuma ya yi addu'ar rahama da gafara ga dukkan muminai da muminai mata da suka riga mu gidan gaskiya.

Bayan haka, Jagoran ya nufi Unguwar Ƙwarbai, inda ya ziyarci ƙabarin marigayi Malam Musa, wanda ya kasance maɗaukin tutar da'awar Shehu Usmanu Ɗanfodiyo zuwa yankin Zazzau, tare da tuna da irin gudummawar da ya bayar wajen hidimar addini.

A ci gaba da wannan ziyarar, Jagoran na Harkar Musulunci a Najeriya ya kai ziyara gidan Madaki Sa'idu da gidan Goggo Hari a Unguwar Magajiya, sannan ya ziyarci gidan Baba Abdulƙadir da ke Ƙwarbai 2, inda ya gana da iyalan waɗannan gidaje.

Har ila yau, Jagoran ya kai ziyara gidan mahaifiyarsa, marigayiya Hajiya Hari Jamo (Allah Ya ƙara mata yarda) da ke Unguwar Jushi a garin Zariya, inda aka tuna da kyawawan halayenta da ayyukan alherin da ta yi wa al'umma.

An gudanar da waɗannan ziyarori cikin yanayi na ƙauna, girmamawa da ruhin addini. A yayin ziyarorin, Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya jaddada muhimmancin ƙarfafa zumunci da haɗin kan al'umma, girmama iyalai, mutunta dattawa da kuma raya tarihin malaman addini da bayin Allah da suka sadaukar da rayuwarsu wajen hidimar Musulunci da al'umma.

Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) Ya Kai Ziyarori ga Dangi da Fitattun Malaman Addini a Zariya

Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) Ya Kai Ziyarori ga Dangi da Fitattun Malaman Addini a Zariya

Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) Ya Kai Ziyarori ga Dangi da Fitattun Malaman Addini a Zariya

Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) Ya Kai Ziyarori ga Dangi da Fitattun Malaman Addini a Zariya

Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) Ya Kai Ziyarori ga Dangi da Fitattun Malaman Addini a Zariya

Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) Ya Kai Ziyarori ga Dangi da Fitattun Malaman Addini a Zariya

Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) Ya Kai Ziyarori ga Dangi da Fitattun Malaman Addini a Zariya

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha